Obasanjo ya ba da shawarwarin yadda za'a magance matsalar tsaro a Najeriya.

Obasanjo ya ba da shawaran yadda za'a magance matsalar tsaro a Najeriya

Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana damuwarsa kan yadda aka dau lokaci mai tsawo domin yaki da Boko Haram a Najeriya fiye da yakin basasar da aka yi a kasar tsakanin 1967 zuwa 1970.

A cewarsa, yakin basasar kasar ya shafe watanni 30 ana gwabzawa, amma an shafe kusan shekaru 15 ana yaki da masu tada kayar baya da masu aikata laifukan ta'addanci a kasar.

Obasanjo ya bayyana haka ne a yayin tattaunawar ‘Toyin Falola’ da aka rika yadawa kai tsaye a kafafen sada zumunta.

Limamin cocin Katolika na darikar Sokoto, Matthew Kukah, da tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Kingsley Moghalu, na daga cikin mahalarta taron yayin tattaunawar.

Da yake amsa tambayoyi kan tashe-tashen hankula, Obasanjo ya ce dole ne shugabanci ya fahimci cewa Najeriya na bukatar hadakar horaswa, kayan aiki, leken asiri, da fasaha don kawo karshen tada kayar baya.

"Akwai muhimman abubuwa guda hudu kuma ina fatan wadanda ke da iko - sojoji, masu zartarwa, da majalisa - sun san abin da suke yi," in ji shi.

“Na farko, akwai horo iri-iri, yakamata a rinka horar da sojoji dabaru iri-iri don yaki da 'yan ta'adda.

“Idan mutanen da kuke mu’amala da su sun zama maƙiya masu wuce gona da iri ko kuma suna zaune a cikin mutane, toh kuna buƙatar horo iri-iri don magance su.

"Daga cikin kasashen da suka yi amfani da irin wannan dabarun Kuma suka yi nasara akwai Kasar Colombia, shin ya kamata mu gayyace su don horar da mutanenmu? 
Ina ganin Babu kunya a cikin hakan, domin horo ne na musamman.

"Haka zalika kayan aikin da za a yi yaƙi a irin wannan yaƙin, ya bambanta da kayan yaƙi na al'ada, ɗayan kuma nazari ne, domin ana buƙatar cikakken fikira, Na hudu shine fasaha.

wadannan hudun dole ne su hadu domin samar da zaman lafiya a cikin kasa.

"Yakin basasa ya dauki watanni 30. Ko da yake muna tunanin zai dauki watanni shida. 
Amma abun takaici wannan yaki da masu tayar da kayar baya da masu aikata manyan laifuka ya shafe kusan shekaru 15."

Obasanjo ya bayyana yadda ya ziyarci Maiduguri a shekarar 2011 domin gano asali, korafe-korafe da kuma shugabancin kungiyar ta Boko Haram.

Obasanjo ya ce tun farko maharan sun ki tattaunawa da gwamnatin tarayya.
Sai daga baya su ka amince da tsagaita bude wuta na kwanaki 21 domin a samu damar tattaunawa.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: