BBC Hausa ta yi bikin karrama gwarazan gasar Hikayata ta bana 2025

BBC Hausa ta yi bikin karrama gwarazan gasar Hikayata ta bana 2025.

Sashen Hausa na BBC ya yi bikin karrama gwarazan gasar Hikayata ta wannan shekaran inda a ka sanar da wadanda suka yi nasara a gasar wacce a ke zaban labarai uku da su ka yi fice a cikin wadanda aka tantance.

Wacce ta yi nasaran zama ta daya a wannan shekaran ita ce Fadhila.

Fadhila marubuciya ce daga jihar Kaduna, kuma matar aure ce mai ƴaƴa uku, sannan ta lashe gasar ne da labarinta mai suna "Tsalle Ɗaya," 

Sannan sai Jamila Lawal Zango wacce ta zo ta biyu da labarinta mai suna "Gobena." 

Sai marubuciya Hafsat Sani Tanko wacce ta zo ta uku da labarinta na mai suna "Samarin Shawo."

Wacce ta zo ta daya ta samun kyautar Naira miliyan 1.

Sai wacce ta zo ta biyu ta samu N750,000

Sai ta uka wacce ta samu Naira N500,000.

Gasar Hikayata, gasa ce wanda sashin hausa na bbc ya fara shiryawa a shekaran 2016 domin bai wa mata damar nuna basirar da Allah ya hore masu wajen rubutu da kirkiran da labari.



SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: