Mummunar hadarin mota yayi sanadiyyar rasuwar mutum 8 a garin Jos

Mummunar hadarin mota yayi sanadiyyar rasuwar mutum 8 a garin Jos

Mutane 8 ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya afku daura da bankin Unity dake kan titin Zaria a garin Jos babban birnin jihar Filato.

Hatsarin ya afku ne da sanyin safiyar yau Alhamis, wanda ya hada da wata tirela da wata motar bas dauke da daliban jami’ar Jos.

Shaidun gani da ido sun ce mutane goma sha daya ne a cikin motar bas din a lokacin da lamarin ya faru.

Rahotanni na cewa mutane bakwai ne suka mutu a take a wurin, sai mutum daya da ya mutu a asibiti, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa takwas.


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: