A ranar laraba ne rundunar sojin Najeriya ta yi bikin Karin girma da karrama manyan hafsoshin soji 28, inda ministan tsaro, Janar Christopher Musa (Rtd) ya bukace su da su tabbatar da daukakarsu ta hanyar aiki tukuru, biyayya da yiwa kasa hidima.
Bikin, wanda aka gudanar a hedkwatar rundunar soji, Mess 1, Asokoro, Abuja, an karrama sojojin masu mukamin Birgediya-Janar su 28, ciki har da daya wanda ya mutu, zuwa mukamin Manjo-Janar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mukaddashin Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Appolonia Anele ya fitar.
Janar Musa, babban bako na musamman, ya yaba wa jami’an bisa jajircewarsu, kwarewa, da sadaukarwa da suka yi na tsawon shekaru.
Ya kuma yi nuni da cewa, Karin girmansu na nuna jajircewarsu wajen tabbatar da tsaron kasa da kuma kokarin hadin gwiwa don karfafa sojojin Najeriya.
"Wadannan jami'an suna daga cikin mafi nagartattun shugabanni a cikin sojojin mu," in ji shi.
Ya kuma yi kira da a kara zurfafa hadin gwiwa tsakanin ma’aikatu, da inganta musayar bayanan sirri, da hadin kai a dukkan hukumomin tsaro, tare da amincewa da goyon bayan iyalan jami’an.
Bikin ya samu halartar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, karamin ministan kudi, ‘yan majalisar dokoki ta kasa, shugabannin masu yiwa kasa hidima, sufeto-janar na ‘yan sanda, da tsaffin hafsoshin tsaro, kwamandojin runduna, kwamandojin cibiyoyin horaswa, da shugaban kungiyar matan hafsoshin sojin Najeriya, da dai sauransu.
A ranar 27 ga Nuwamba, 2025 ne aka amince da karin girma ga jami’an sojin, inda a ka Kara ma Birgediya Janar 28 matsayi zuwa Manjo Janar da Kuma masu mukamin Kanar su 77 zuwa Birgediya Janar.

0 Comments:
Post a Comment