Fubara ya bayyana sauya shekar sa ne a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Fatakwal a ranar Talata.
Gwamnan jihar Ribas ya bi sahun gwamnan jihar Delta Sheriff Oborevwori; Gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno; Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah; da takwaransa na Bayelsa, Duoye Siri, wadanda dukkansu sun fice daga jam’iyyar adawa ta PDP.
Da yake jawabi a wurin taron, gwamnan ya ce, “Ba za mu iya goyon bayan shugaban kasa (Tinubu) ba idan har ba mu yi cikakken mubayi'a ba, ba.
“Don haka mun yanke wannan shawarar ce a nan a yau, cewa duk wanda ya bi ni kuma ya sha wahala tare da ni, shawarar da yammacin yau ita ce za mu koma APC.”
Ficewar tasa ta zo ne bayan ya ziyarci shugaban kasa Bola Tinubu a fadar gwamnati da ke Abuja ranar Litinin.
Rahotanni sun ce ya isa fadar shugaban kasan da misalin karfe 5:01 na yamma a wancan ranar, kafin daga bisani jami’in hulda da manema labarai na fadar shugaban kasar ya yi mashi rakiya zuwa ofishin shugaban.

0 Comments:
Post a Comment