Mohamed Salah ya zargi Liverpool da yin watsi da shi

Mohamed Salah ya zargi Liverpool da yin watsi da shi

An cire sunan dan wasan gaba na Liverpool, Mohamed Salah daga cikin jerin ‘yan wasan da za su buga wasan da Liverpool za ta yi da Inter Milan a gasar zakarun Turai a yau Talata. 
 
Matakin da kulob din ya dauka na cire Salah daga cikin 'yan wasan ya zo ne bayan da ya yi wata tattaunawa da yan jaridu a ranar Asabar, inda ya yi ikirarin cewa Kungiyar ta Liverpool ta jefar da shi gefe daya, saboda yanayin rashin nasarorin da kungiyar ta shiga, kuma ya ce dangantakarsa da kocin Kungiyar, Arne Slot ta tabarbare.
 
Da yake magana a Milan gabanin wasan, Slot ya ce ba ya jin haka wani abun damuwa ne, kuma ya yi mamakin kalaman Salah, yayin da kuma ya musanta lamarin cewa ya yi masa zagon kasa.
 
Majiyoyi sun shaida wa kafar yada labarai ta BBC Sports cewa ba za a dauki matakin ladabtarwa a kan Salah ba.

Kuma dan wasan mai shekaru 33 yana shirin tashi zuwa gasar cin kofin nahiyar Afrika a ranar Litinin mai zuwa, kuma da alama ba zai buga wasan Liverpool da Brighton ranar Asabar ba.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: