Ƙasar Iran ta sanar da dakatar da hare-haren soji da take kai wa Isra’ila, tana mai cewa dakarunta sun gudanar da martani mai ƙarfi game da Hare-haren da Israi'la ke kai Lebanon, tare da gargadin cewa duk wani sabon rikici zai iya haifar da sake ɗaukar matakan soji.
A wata sanarwa da rundunar tsaron Iran ta fitar a yau Litinin, ta ce an dakatar da ayyukan sojin ne bayan wasu hare-haren makamai masu linzami da aka kai kan wasu wuraren sojin Isra’ila.
Mahukuntan Iran sun bayyana cewa an kai hare-haren ne a matsayin martani ga ayyukan sojin Isra’ila a kudancin Lebanon da kuma yankunan kudancin Beirut.
Sun kuma ce an kai hare-haren kan wasu sansanonin jiragen saman sojin Isra’ila da Tehran ke zargin suna da hannu a hare-haren da ake kai wa Lebanon.
Sanarwar ta ce dakatar da ayyukan sojin ba yana nufin Iran ta rage shirin kare kanta, tana mai jaddada cewa dakarunta suna cikin cikakken shiri idan rikici ya sake barkewa.
Mai magana da yawun hedikwatar rundunar, Birgediya Janar Ebrahim Zolfaghari, ya ce dakarun Iran sun nuna cikakken ƙarfin kai hari da kuma kare kai a lokacin farmakin. Ya yi gargadin cewa duk wani sabon hari kan Iran ko ƙawayenta a yankin zai fuskanci martani mafi tsauri.
Iran ta kuma zargi Amurka da goyon bayan Isra’ila a rikicin yankin, tana mai cewa Amurka na da alhakin ƙaruwar tashin hankalin da ake gani a halin yanzu.
Iran ta sake jaddada matsayinta cewa zaman lafiya a yankin zai samu ne idan aka dakatar da ayyukan soji a Lebanon tare da mutunta yarjejeniyoyin tsagaita bude wuta da ake da su.
Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar tashin hankali a Gabas ta Tsakiya, inda hare-haren da ake musayarwa tsakanin bangarori daban-daban suka kara haifar da fargabar yiwuwar rikicin ya bazu zuwa wasu sassan yankin.
Duk da cewa Iran ta ce ta dakatar da hare-haren da take kaiwa a yanzu, jami’anta sun bayyana cewa za su ci gaba da sanya ido kan halin da ake ciki, kuma duk wani mataki na gaba zai dogara ne da yadda al’amura za su gudana.
Sabbin abubuwan da suka faru sun kara nuna ci gaba da takun-saka tsakanin Iran da Isra’ila, yayin da kowanne bangare ke zargin ɗayan da haddasa rashin zaman lafiya da matsalolin tsaro a yankin.