Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, na jam’iyyar Accord, ya lashe kananan hukumomi 19 daga cikin 30 na jihar a zaben gwamnan da aka gudanar ranar Asabar.
A daya bangaren, dan takarar jam’iyyar APC, Bola Oyebamiji, ya samu nasara a kananan hukumomi 11.
Adeleke na jiran Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta yi sanarwar karshe bayan kammala tattarawa da tantance sakamakon zaben a ranar Lahadi.
Jam’iyyun siyasa 15 ne suka shiga takarar, sai dai manyan fafatawar ta fi kasancewa tsakanin jam’iyyar Accord ta Adeleke da APC.
Dan takarar African Democratic Congress (ADC), Najeem Salaam, ya zo na uku da tazarar kuri’u mai yawa, inda ya samu kuri’u 14,989.
Ana sa ran jami’in da ke kula da sanar da sakamakon zaben, Mataimakin Shugaban Jami’ar Tarayya, Oye-Ekiti, Farfesa Joshua Ogunwole, zai bayyana wanda ya yi nasara a cibiyar tattara sakamakon INEC da ke Osogbo.
Yadda zaben ya kasance:
Adeleke ya samu gagarumar nasara a kananan hukumomi da dama, ciki har da Ede South, Ife North, Ife Central, Osogbo, Ife East, Ifelodun, Iwo da Ede North.
A gefe guda kuma, Oyebamiji na APC ya samu nasara a kananan hukumomi kamar Ilesa East, Boripe, Irepodun, Irewole, Atakumosa West, Atakumosa East, Olaoluwa, Ife South da Olorunda.
Sakamakon ya nuna cewa an samu gasa mai tsauri a wasu kananan hukumomi, inda bambancin kuri’un da aka samu tsakanin ‘yan takarar ya kasance kadan a wasu wurare.
Dubban masu kada kuri’a da aka tantance sun fito rumfunan zabe daban-daban domin kada kuri’unsu a kananan hukumomi 30 na jihar.
Ana sa ran INEC za ta tabbatar da wanda ya lashe zaben gwamnan Jihar Osun a hukumance bayan jami’in zaben ya kammala sanar da sakamakon karshe.

0 $type={blogger}:
Post a Comment