Abubakar Ladan wanda aka fi sani da Abubakar Ladan Zariya, ya kasance shahararren mawaƙi, marubuci, malami, da Adabi, daga Arewacin Najeriya.
Ya tsaya sosai wajen raya harshen Hausa ta hanyar waƙa, rubuce-rubuce, da kuma koyarwa.
An haifi Abubakar Ladan a Zariya, jihar Kaduna, a shekarar 1937. Ya yi makarantar allo da ta boko tun yana yaro.
Tun yana ƙarami yake nuna baiwa ta yin waƙa da rubutu, musamman na addini da tarbiyya.
Ya yi aiki a fannoni da dama, ciki har da Malanta da aikace-aikacen gwamnati.
Daga baya ya shiga harkar adabi kai tsaye, yana rubuce-rubuce da waƙar zamani da ta gargajiya.
Ya shahara a matsayin mawaƙin addini, musamman kan karantar da jama’a darussa ta hanyar zance da baituka.
Abubakar Ladan ya rubuta littattafai da waka da dama. Fitattun ayyukansa sun haɗa da:
Wakar Buhari da Idi
Wakar Nijeriya
Rubuce-rubucen tarbiyya da na tarihi masu yawa
Waƙa
Waƙoƙinsa sun shafi:
Addini
Siyasa
Tarbiyya
Gina haɗin kai
Rayuwar al’umma
Waƙoƙinsa sun kasance cikin tsari na baiti da kari, kuma ana yawan amfani da su wajen koyar da yara a makarantu saboda sauƙin fahimta da zurfin ma’ana.
Ya kasance da salo na hikima, nuni, da gargaɗi.
Ya yi amfani da harshen Hausa cikin tsabtatacciyar hanyar gargajiya.
Ya taimaka wajen raya adabin zamani, har ya zama ɗaya daga cikin tubalan adabin Hausa.
Malamai da ɗalibai a jami’o’i suna nuna shi a matsayin misali kan yadda ake waƙar Hausa ta zamani.
Abubakar Ladan ya rasu a 2015, ya bar babban tarin ilimi da adabi da ake ci gaba da amfani da shi har yanzu.
Dr. Tsiga

0 Comments:
Post a Comment