Sanin hakikanin Albashin Masu rike da mukaman siyasa a Najeriya batu ne da ake yawan tafka muhawara da cece kuce akan shi saboda da zarginsu da Al'ummar Kasar Ke yi na wawure kaso mai tsoka a bangaren kasafin kudin Kasar domin rarrabawa kawunansu, duk da cewa a lokuta da dama Yan majalisun da sanatoci sunsha karyata zargin yayin da wasunsu ke fasa kwai.
A wannan rahoton zamu Ji yadda danbarwar Albashin Yan majalisun yake da kuma shin menene gaskiyar yadda ake Ba kowane dan majalisan tarayya da na jihohin Kasar.
Idan ba'a manta ba a farkon wannan makon ne Tsohon Shugaban Kasar Olusegun Obasanjo ya bayyana Yan majalisar kasar da cewa suke tsara ma kansu da kansu albashi Mai yawa da kuma hanyoyin da suke samu kudi fiye da kima. lamarin dai ya janyo kace nace inda majalisar ta mayar masa da martani bada jimawa ba, tana Mai fassara kalamun nashi a matsayin mara tushe balle makama.
Haka zalika Shima Sanata Lawal Adamu Usman danmajalisa da ke wakiltar Kaduna ta tsakiya a Majalisar dattawan kasar ya shaida wa Kafar watsa labarai na BBC hausa tare da rantsewa cewa "albashinsu bai kai miliyan daya ba a wata.
‘’Duk albashinmu gabadaya bai kai miliyan daya ba wallahi, idan kuma maganar alawus-alawus ne za a yi, sai dai mu ciyo bashi, saboda girman zirga-zirgar da nake yi daga Abuja zuwa mazaɓun da nake wakilta domin kowa na zuwa da buƙatarsa," in ji sanatan.
Sai dai kasa da mako daya da yin wannan maganar Sai ga shi sanata.
Abdulrahman Kawu Sumaila dan majalisa mai wakiltar Kano ta kudu a majalisar dattijan ya fito fili ya bayyana cewa an turo mashi da naira miliyan 21 a matsayin alawus dinshi na sanata Kamar yadda jaridar daily trust ta ruwaito inda ya kara da cewa bai san Ko nawa shuwagabannin majalisun Masu rike da mukami su 10 ke kwasa ba a halin yanzu.
Don haka maganar Albashin Dan majalisa da na sanatoci duk Wanda yace ga iya yawan kudaden da suke samu za'a iya cewa yayi Karya domin gundarin albashinsu ba shi bane kadai abun da suka samu, hatta hutu idan majalisa zata tafi akwai alawus da ake waike ma kowane dan majalisa.
Article Translation in English Language.
Knowing the actual salaries of political office holders in Nigeria is a subject that is often debated and argued over because of their accusations that the people of the country are stealing a large portion of the country's budget to distribute their among themselves, even though in Many times, members of parliament and senators have denied the allegations while some of them are cracking eggs.
In this report, we will hear how the Salary of the Members of Parliament is and what is the truth of how each member of the federal and state parliaments of the country is paid.
If we don't forget, earlier this week, the former President Olusegun Obasanjo told the members of parliament that they are setting high salaries for themselves and the ways in which they earn excessive amounts of money.
The situation led to the fact that the parliament responded to him shortly, interpreting his words as baseless.
Likewise, Senator Lawal Adamu Usman, the member of parliament representing Kaduna Central in the Senate of the country, told the BBC Hausa media and swore that "their salary is less than one million a month.
"Our total salary is less than one million, by the way, if we are going to talk about allowances, we will have to go into debt because of the amount of traffic that I do from Abuja to the constituencies that I represent because everyone comes with their needs." said the senator.
But less than a week after making this statement, the senator. Abdulrahman Kawu Sumaila, the member of parliament representing Kano South in the senate has come out and stated that he was sent 21 million naira as a senatorial allowance.
Therefore, talking about the salaries of members of parliament and senators, anyone who says that they can earn a lot of money can be said to be lying because their salary is not the only thing they get, even when the parliament goes on vacation, there is an allowance that is sent to every member of parliament.
0 Comments:
Post a Comment