kiristoci 600,000 ne ke zaune a sansanin 'yan gudun hijira ta IDP a jihar Benuwe, inji Riley Moore

 kiristoci 600,000 ne ke zaune a sansanin 'yan gudun hijira ta IDP a jihar Benuwe, inji Riley Moore

Dan majalisar dokokin Amurka Riley Moore, ya ce kiristoci 600,000 ne ke zaune a sansanin 'yan gudun hijira ta IDP a jihar Benuwe.

Ya kuma bayyana yadda ake cin zarafin al’ummar Kirista a jihar ta Benue, inda ya ba da labarin abin da aka fada masa a ziyarar da ya kai sansanin ‘yan gudun hijira ta IDP.

A cewar dan majalisar, wadanda ya zanta da su sun bayyana mashi hare-haren da suka yi sanadin mutuwar iyalansu baki daya tare da tilasta wa wadanda suka tsira da rayukansu barin kauyukansu.

"Sun faɗi labarai masu ban tsoro da za su kasance tare da ni har tsawon rayuwata," inji Dan Majalisar.

Ya ba da misali da yadda wata mata ta ce, “an tilasta mata kallon yadda suke kashe mijinta da ‘ya’yanta biyar. 

Inda Ita da dan cikinta da kyar suka tsira.”

Ya kara da cewa, wata mata, ta gaya masa "an kashe danginta a gabanta kuma an akai sanadin fitan jaririnta daga cikinta."

Moore ya kuma bayyana wani mutum wanda ya ce "an yi wa danginsa kaca-kaca a idonsa har lahira kuma aka lalata masa hannun shi.

Dan majalisar ya bayyana cewa “fiye da kiristoci 600,000” a halin yanzu su ke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira a jihar Benuwe, yankin da ya sha fama da rikici na tsawon shekaru tsakanin al’ummomin manoma da kungiyoyin masu dauke da makamai.

"Ya kamata waɗannan Kiristoci su zauna a ƙasar kakanninsu ba tare da tsoron Fulani masu kisan kiyashi ba," Moore ya rubuta, yana mai kira ga al'ummar duniya da a mai da hankali kan rikicin.

A baya dai Moore ya wallafa cewa ya gana da shugabannin Tiv da na Katolika a ziyarar da ya kai jihar.

“Abin alfahari ne kuma mai matukar burgewa na gana da Mai Girma Bishop Wilfred Anagbe, Bishop Isaac Dugu, da kuma Mai Martaba James Ioruza, sarkin gargajiya na kabilar Tiv, domin tattauna batun kisan kiyashin da Fulani ke ci gaba da yi a jihar Binuwai.

Ya kara da cewa Amurka ba za ta yi watsi da abubuwan da al'ummomin yankin suka yi ba.



SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: