Gwamnatin Burkina Faso ta kama wani Jirgin saman sojin Najeriya tare da yin gargadin harbo duk wani jirgin sama da ya sake yin shawagi a sararin samaniyar kasar ba bisa izini ba.
Gwamnatin Burkina Faso ta ce wani jirgin saman sojin Najeriya dauke da sojoji 11 yayi saukar gaggawa a kasar a ranar Litinin, bayan da ta ce ya keta hurumin sararin samaniyar kasar.
kamfanin dillancin labaran gwamnatin kasar ne ya wallafa wata sanarwa a shafinsa na yanar gizo.
Wasu bayanai sun ce jirgin Sojin saman na Najeriya wanda bana yaƙi ba ne ya yi saukar gaggawa a cikin Burkina Faso sakamakon tangarɗar da ya gamu da ita.
Sanarwar wadda aka fassara daga harshen Faransanci ta ce, “Kungiyar Kasashen Sahel AES, wacce ta hada Kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar ta sanar da cewa wani jirgin sama kirar C130 mallakar rundunar sojojin saman Tarayyar Najeriya yayi saukar gaggawa a yau 8 ga watan Disamba, 2025, a Bobo Dioulasso na kasar Burkina Faso, biyo bayan wani yar tangarda da Jirgin ya samu a yayin da yake sararin samaniyar kasar ta Burkina Faso.
Sanarwar ta ce Jirgin sojin yana da matuka 2 da fasinjoji 9 a cikin shi.
Sanarwar ta kara da cewa, binciken da hukumomin kasar Burkina Faso suka gudanar ya nuna rashin ba da izinin shawagi a sararin samaniyar Burkina Faso ga wannan Jirgin.
Hukumar ta AES ta yi Allah-wadai da lamarin a matsayin cin zarafi ga 'yancin kai, da keta dokar kasa-kasa, tana mai cewa "ta yi Allah-wadai da kakkausan lafazi da wannan keta sararin samaniyarta da kuma ikon mallakar kasashe mambobinta."
Hukumar ta yi gargadin cewa "Kasashen na cikin shirin ko ta kwana a ko da yaushe domin kare ikon sararin samaniyarsu… kuma an ba hukumomi izinin kakkabo duk wani jirgin da zai keta sararin samaniyar Kasashen ba tare da izini ba"
Kawo yanzu dai babu wani bayani daga hukumar sojin saman Najeriya ko kuma gwamnatin tarayya.
Matakin kame wannan jirgi da fasinjansa na nuna yiwuwar dawowar tsamin alaka tsakanin Najeriyar da hadakar ta AES wadanda suka fice daga ƙungiyar ECOWAS bayan juyin mulkin da Sojoji suka yi a Kasashen.

0 Comments:
Post a Comment