Sabon kamfanin zirga-zirgan jirgin sama na "Binani Air" zai fara gudanar da harkokin kasuwancinsa a ranar Litinin mai zuwa tare da fara zirga-zirgar jirage a Jihohin Anambra, Legas, Kano, Maiduguri, da Fatakwal.
Kamfanin jirgin wanda ya karbi takardar shedar fara aikinsa na zirga-zirgan jirage wato (Air Operating Certificate (AOC) a turance) tun a watan Yulin shekarar 2024, mallakin Sanata Aishatu Binani ce, wadda ake yi wa kallon macen da ta fi kowace mace kudi a jihar Adamawa da ma Arewa maso Gabas.
Ta kuma mallaki gidan buga littattafai mafi girma a Arewacin Najeriya.
Kamfanin jiragen sama na Binani ya zama na farko a tarihi a matsayin kamfanin jirgin sama na farko a Najeriya mallakin mace.

0 Comments:
Post a Comment