'Yan bindiga sun kai hari a wani cocin dake jihar Kogi, inda suka yi garkuwa da Fasto da wasu masu ibada.
Gwamnatin jihar Kogi ta tabbatar da harin da aka kai da sanyin safiyar yau lahadi a wani cocin Cherubim da Seraphim da ke Ejiba a karamar hukumar Yagba ta yamma a jihar.
Kwamishinan yada labarai na jihar Kingsley Fanwo ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar yau Lahadi a Lokoja, inda ya yi kakkausar suka ga lamarin.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, ‘yan bindigar da suka kaddamar da harin, sun yi garkuwa da faston da matarsa da wasu masu ibada.
Harin ya jefa al’ummar Ejiba cikin firgici, inda rahotanni suka ce mazauna garin sun tsere domin neman tsira.

0 Comments:
Post a Comment