‘Yan bindiga sun bukaci a biya su naira N150m domin su sako basaraken da suka sace a jihar Kwara.

‘Yan bindiga sun bukaci a biya su naira N150m domin su sako basaraken da suka sace a jihar Kwara.

‘Yan bindigan da suka yi garkuwa da basaraken nan, Ojibara na Bayagan a karamar hukumar Ifelodun a jihar Kwara, Alh Kamilu Salami, a gonarsa da safiyar ranar Asabar, sun bukaci al’umma da su kai Naira miliyan 150 kafin su sako shi.

Rahoton da muka samu na cewa ‘yan bindigar sun tattauna da al’umma da sanyin safiyar ranar lahadi domin neman kudin.

‘Yan fashin sun bukaci Oba Ojibara da ya tattauna da jama’ar yankinsa domin su amince yana hannunsu.
Sarkin yayi waya da Al'ummarsa inda cikin kuka, ya bukaci su kawo masa dauki ta hanyar tattaunawa da 'yan fashin dajin domin a sako shi cikin gaggawa.

Ya ce sun dauke shi a kan babur sama da sa’o’i 5 a cikin dazuzzuka masu sarkakiya kafin su isa inda suke, inda suke tattaunawa da al’umma.

Har zuwa lokacin da aka rubuta wannan rahoton dai ba a fara tattaunawa ba, domin an yi kiran ne domin a sanar da al’umma adadin kudin fansa da kuma sarkin na hannunsu.

Rahotanni sun ce Sarkin ya shaida wa al’ummar yankinsa cewa an kuma sace wasu mutanen da ba a tantance adadinsu ba a unguwar da ke makwabtaka da su, yayin da ake dauke da shi.

Garin Bayagan babban gari ne dake karamar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara.
'Yan bindigan dai sun yi garkuwa da sarkin ne da misalin karfe 9:30 na safiyar ranar asabar, inda suka kai hari a gonarsa da bindigogi kirar AK-47.


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: