Ilhan Omar ta yi Allah wadai da kalaman Shugaban Amurka Donald Trump akan 'yan Somalia

Ilhan Omar ta yi Allah wadai da kalaman Shugaban Amurka Donald Trump akan 'yan Somalia

Ilhan Omar ta yi Allah wadai da kalaman Shugaban Amurka Donald Trump inda ya kira bakin haure daga Somaliya a matsayin ‘sharar gida’.

Yayin wani taron majalisar ministocin a ranar Talata, Trump ya nuna wariyar launin fata, yana mai bayyana Omar da sauran bakin haure daga kasar Somaliya a matsayin "sharar gida" tare da yin kira gare su da su bar Amurka.

Da take mayar da martani ga Trump, Omar ta rubuta a shafunta na sada zumunta cewa "Rashin sha'awarsa da ni yana da ban tsoro." "Ina fatan ya sami taimakon da yake bukata."

A ‘yan makonnin da suka gabata Trump ya kara zafafa kalamansa na nuna kyama ga bakin haure, musamman bayan wani mummunan harbin da aka kai wa wasu dakarun tsaron kasa biyu a birnin Washington, DC, a watan jiya.

Wanda ake zargi da harin dan kasar Afganistan ne da yayi gudun hijira daga kasar a shekarar 2021, bayan janyewar sojojin Amurka da na kawancen kasashen waje. 

Trump ya yi amfani da harin a matsayin ginshikin tsaurara hana bakin haure shiga Kasar daga Kasashe da ya bayyana a matsayin "masu tasowa", ciki har da Somaliya.


"Za mu bi hanyar da ba ta dace ba idan muka ci gaba da kwaso shara zuwa cikin kasarmu. Ilhan Omar shara ce, shara ce, kawayenta shara ne," in ji shugaban na Amurka.

"Waɗannan ba mutanen da suke aiki ba ne. Waɗannan ba mutanen da suke cewa, 'Mu je, mu zo. Bari mu mai da wannan kasar mai girma. 

'Waɗannan mutane ne da ba su yin komai sai gunaguni. Suna gunaguni, kuma daga inda suka fito, ba su samar da komai ba."

Trump ya ce sam bai san Ilha Omar ba amma yana kallon yadda take korafin game da Amurka tsawon shekaru. 

"Ina tsammanin ita mutum ce da ba ta da kwarewa. Ita muguwar mutum ce ta gaske," in ji shi.


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: