‘Yan majalisar dokokin Amurka a ranar Talata sun soki gwamnatin Najeriya kan gazawarta wajen dakile karuwar tashe-tashen hankula da kashe-kashe da ake yi a fadin kasar.
An bayyana hakan ne a yayin wani taron hadin gwiwa na kwamitin kasafin kudi na Majalisar Dokokin Amurka, wanda aka yi domin nazarin zarge-zargen kai hare-hare a kan kiristoci da sauran kungiyoyi masu rauni a Najeriya.
Da suke jawabi a zaman, ‘yan majalisar sun yi tsokaci game da sake ayyana Najeriya da Donald Trump ya yi a matsayin kasar da ke nuna fifiko akan wani bangare na Addini da kuma gargadin da ya yi na daukan matakin soji idan ba'a daina kashe Kiristoci a kasar.
Dan majalisa Chris Smith ya ce hukumomin Najeriya na gazawa wajen gudanar da aikin da tsarin mulki ya ba su na kare 'yan kasa.
Inda ya kara da cewa "Wadanda suka kai wadannan hare-haren suna ci gaba da aiwatar da su ba tare da wani hukunci ba," kamar yadda ya shaida wa kwamitin.
Danmajalisa Brian Mast yana goyon bayan Trump game da kudinsa akan Najeriya, yana mai jaddada cewa dole ne Washington ta kara matsa lamba akan hukumomin Najeriya.
Ya bukaci Amurka da ta tabbatar an kwace makaman dake hannun kungiyoyin masu dauke da makamai, sanna a maido da al'ummomin da suka rasa matsugunansu, da kuma gurfanar da wadanda ke da alhakin kai hare-haren.
Har ila yau, da yake magana, Riley Moore, mataimakin shugaban majalisar wakilai na reshe na majalisar dokoki kuma jigo mai fafutukar kare hakkin addini, ya sake nanata da'awar kisan kiyashi a Kan Kiristoci.
Inda ya ce "Duniya ba za ta zura ido ta bar abin da ke faruwa da Kiristoci a Najeriya ba."

0 Comments:
Post a Comment