A ranar Juma'a ne da daddare hukumar kwallon kafa ta duniya ta fitar da jadawalin gasar cin kofin duniya na badi 2026 wanda za'a gudanar a Kasashen Amurka da Kanada da Mexico.
Inda bikin ya samu halartan manya- manyan baki ciki harda shuwagabannin Kasashen da za'a gudanar da gasar.
Haka zalika FIFA ta ba Shugaban Amurka Donald Trump kyautar Lambar yabo ta zaman lafiya a lokacin bikin, inda Shugaban FIFA Inferntino ya sanar da cewa a bashi kyautar lambar yabon ne saboda rawan da ya taka wajen kawo karshen yakin da Israi'la ta yi a Gaza.
Kyautar ta kasance irinta ta farko da hukumar ta samar wacce ake ma kwallon a ba shi ne sakamakon rashin samun kyautar lambar yabon ta zaman lafiya ta "Nobel Peace Prize" 2025 wacce ya nuna muradin samu a fili karara.
Ga yadda tsarin jadawalin ya kasance.
Rukunin A:
Mexico
Afirka ta Kudu
Koriya ta Kudu
Ƙasar da za ta fito a wasan cike gurbi na Uefa rukunin D
Rukunin B:
Canada
Qatar
Switzerland
Ƙasar da za ta fito a wasan cike gurbi na Uefa rukunin A
Rukunin C:
Brazil
Moroko
Scotland
Haiti
Rukunin D:
Amurka
Paraguay
Australia
Ƙasar da za ta fito a wasan cike gurbi na Uefa rukunin C
Rukunin E:
Germany
Ivory Coast
Ecuador
Curacao
Rukunin F:
Netherlands
Japan
Tunisia
Ƙasar da za ta fito a wasan cike gurbi na Uefa rukunin B
Rukunin G:
Belgium
Egypt
Iran
New Zealand
Rukunin H:
Spain
Saudi Arabia
Uruguay
Cape Verde
Rukunin I:
France
Senegal
Norway
Ƙasar da za ta fito a wasan cike gurbi na Fifa rukunin 2
Rukunin J:
Argentina
Algeria
Austria
Jordan
Rukunin K:
Portugal
Uzbekistan
Colombia
Ƙasar da za ta fito a wasan cike gurbi na Fifa rukunin 1
Rukunin L:
England
Croatia
Panama
Ghana.

0 Comments:
Post a Comment