An sako wasu ‘yan Najeriya uku da aka tsare a kasar Saudiyya tun watan Agustan 2025

 
An sako wasu ‘yan Najeriya uku da aka tsare a kasar Saudiyya tun watan Agustan 2025

An sako wasu ‘yan Najeriya uku da aka tsare a kasar Saudiyya tun watan Agustan 2025 bayan hukumomin Saudiyya sun tabbatar da cewa ba su da alaka da yunkurin safarar haramtattun abubuwan da aka samu a jakunkunan su a filin jirgin sama na Sarki Abdul Aziz dake Jeddah.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, Kimiebi Ebienfa ne, ya tabbatar da sakin nasu a wata sanarwa da ya fitar jiya Laraba.

Sanarwar ta kara da cewa, “Ma’aikatar Harkokin Waje ta hannun karamin ofishin jakadancin Najeriya a Jeddah, ta samu sakin tare da dage haramcin tafiye-tafiye da aka yi wa wasu ‘yan Najeriya uku: Abdulhamid Sadieq, Maryam Hussein Abdullahi, da Bahijah Aminu Abdullahi, wadanda aka kama a watan Agustan 2025 a filin jirgin sama na Sarki Abdul Aziz dake Jeddah, Saudi Arabia.

Sanarwar ta bayyana cewa, an kama mutanen uku ne bayan da aka gano haramtattun abubuwa a cikin jakunkunan su, wanda daga baya aka fahimci cewa kungiyoyin masu aikata laifuka ne suka yi amfani da tikitinsu su, inda su ka saka masu haramtattun kayan a jakunkunan su a filin jirgin saman Malam Aminu Kano da ke Kano ba tare da saninsu ba.



SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: