Kungiyar kwallon kafar Manchester City ta lallasa babbar abokiyar hamayyarta Manchester United da ci 3-0 a filin wasa na Etihad a wasan Premier league mako na 4.
Fil Foden shine Wanda ya fara zura kwallon farko a ragar United a mintuna na 18 da fara wasan kafin Ealing Haaland ya zura kwallo ta biyu da ta uku bayan an dawo hutun rabin lokaci a mintuna na 53 da 68.
Yanzu Manchester City ta koma mataki na 8 a teburin na premier league da maki 6 yayin da United ta koma mataki na 14 da maki 4.
0 Comments:
Post a Comment