Dubun dubatan Mutane a New Zealand sun fito zanga-zangar adawa da kisan gillar Israi'la a Gaza

 
Dubun dubatan Mutane a New Zealand sun fito zanga-zangar adawa da kisan gillar Israi'la a Gaza

Dubun dubatan Masu Mutane ne suka fito zanga-zangar nuna goyon bayan Falastinawa a birnin Auckland na kasar New Zealand inda suka yi kira ga Kasashen duniya da su kakaba wa Israi'la takunkumi sakamakon kisan gillar da take cigaba da yi a Gaza.

Hare-haren Israi'la a Gaza ya kara kamari ne tun bayan ayyana shirinta na mamaye birnin gaba daya.

Zuwa yanzu dai a kalla mutane 64,803 Israi'la ta kashe tare da raunata 164,264 a Gaza tun bayan harin 7 ga watan Oktoban 2023 da Kungiyar Hamas ta kai cikin Israi'la. 

An Kuma yi imanin cewa wasu dubbai na karkashin baraguzan ginin. 

Mutane 1,139 aka kashe a harin da Hamas din ta kai Isra'ila a ranar 7 ga Oktoba, tare da yin garkuwa da mutun 200.


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: