Dan wasan Brentford, K. Schade ne ya fara zura kwallon farko a ragar Chelsea a mintuna na 35 da fara wasan, sai dai bayan an dawo hutun rabin lokaci Chelsea ta samu nasaran farke kwallo a mintuna na 61 ta hannun Dan wasan gabanta Cole Palmer, kafin daga bisani Chelsea ta zaru kwallo ta biyu a mintuna na 85 Wanda Caicedo ya zura. Sai dai murna ta koma ciki ga Chelsea inda Brentford din ta farke kwallon bayan an Kara lokacin tashi daga wasan a mintuna na 90+5 inda F. Carvalho ya zura kwallon.
Haka zalika a sauran wasannin da aka buga a Ranar Asabar din Kungiyar Kwallon kafar Arsenal ta lallasa ta Nottingham Forrest da ci 3-0.
Yayin da Tottenham hospurt ta doke Westham United da ci 3-0, sai Fulham wacce ta doke Leeds United daci 1 mai ban haushi, ita ma Newcastle United ta samu nasaran doke Wolverhampton da ci 1-0, yayin da AFC Bournemouth ta doke Brighton 2-1 sai Crystal Palace da Sunderland Wanda suka tashi 0-0 kamar yadda Everton da Aston Villa suka tashi wasansu.
0 Comments:
Post a Comment