Justin Kluivert ya kafa tarihi a matsayin dan wasan da ya fara zura kwallaye 3 a bugun fanareti a tarihin gasar Premier league.
Dan wasan kungiyar kwallon kafar Bournemouth, Justin Kluivert ya karbi kyautar shaidar "Guinness World Record" a matsayin dan wasa farko da ya taba zura kwallo 3 a bugun fanareti a tarihin gasar Premier league.
An bashi shaidar ne a lokacin karawar Kungiyarsa ta Bournemouth da Brighton a Ranar Asabar da ta gabata.
Dan wasan Wanda da ne ga tsohon dan wasan Barcelona da kasar Netherlands Patrick Kluivert, ya samu wannan nasaran ne a ranar 30 ga watan nuwanban shekara 2024 a wasan da Bournemouth din ta doke Wolverhampton da ci 4-2 a gasar Premier league in da ya zura kwallaye har guda uku a bugun daga kai sai mai tsaro gida (fanareti).
Tun da aka fara gasar Premier league ba'a taba samun dan wasa da yi hakan ba.
0 Comments:
Post a Comment