Hukumar jin dadin Alhazai ta kasa NAHCON ta umurci maniyata aikin hajjin bana 2026 su biya kudin aikin hajjin da wuri.
Hukumar alhazai ta kasa ta bayyana damuwarta kan jinkirin biyan kudin aikin hajjin bana 2026 domin shirya maniyyata, tana mai cewa hakan na iya kawo tsaiko wajen samar da masauki a wurare masu kyau a Makka da Madina.
Shugaban Hukumar Farfesa Abdullahi Saleh-Usman ne ya bayyana haka a Katsina a ranar Larabar da ta gabata, yayin da ya jagoranci tawagar da suka kai ziyarar ban girma ga Gwamna Dikko Radda.
Saleh-Usman ya ce ziyarar da ya kai wa gwamnan yayi ta ne domin neman goyon bayan sa a matsayinsa na shugaban kungiyar gwamnonin Arewa maso Yamma, domin a samu saukin biyan kudin akan lokaci.
Ya kuma bayyana batun tallafin shugaban kasa na aikin Hajjin 2024 a matsayin daya daga cikin nasarorin da hukumar ta samu a karkashin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
0 Comments:
Post a Comment