Masu aikin ceto a Indonesia sun gano tarkacen jirgin saman da yayi hatsari dauke da mutane 11.
Masu aikin ceto a Indonesiya sun gano tarkacen jirgin saman da ya bace da ake kyautata zaton ya yi hatsari da mutane 11 a cikinsa a lokacin da yake tunkarar wani yanki mai tsaunuka a tsibirin Sulawesi a lokacin da ake cikin yanayin hadari.
An gano karamin jirgin ne - wanda ke kan hanyarsa daga Yogyakarta na tsibirin Java dake Indonesia zuwa Makassar, babban birnin lardin Sulawesi ta Kudu - bayan ya bace ranar Asabar.
Jirgin mai lamba Turboprop ATR 42-500, yana aiki ne da jiragen saman Indonesiya, kuma an gano shi ne a yankin Leang-Leang da ke Maros, wani yanki mai tsaunuka na lardin Sulawesi ta Kudu dake Kasar ta Indonesiya.

0 Comments:
Post a Comment