Tarihin Sheikh Albani Zaria
An haifi Ash-Sheikh Albani Zaria ne a watan Rabiu Thani 1379 dai dai da 27 Sept 1960, a cikin garin Muchia dake Sabon Garin Zaria a Jihar Kadunan Najeriya.
Malam ya taso tun yana yaro da son ilimi kamar yadda wani malamin shi ya siffanta shi da cewa: “Albaniy tun yana 'Karami da angan shi ina kaje; karatu, ina zaka; karatu, me kake yi; karatu, me ka gama; karatu.
Mahaifiyarshi mai Suna Saudatu ita ta fara bashi 'karfin guiwar karatun addini na musamman, domin itace wadda ta fara siyar da akuyarta tabashi kudin ya siyo littafin Saheehu Muslim nashi na farko. Har ila yau mahaifiyarshi ta taba 'daukan shi tun yana 'karami ta kaishi gurin wasu malamai a cikin garin Kano domin su karantar dashi Karatun addini da zummar cewa 'danta ya zama Malami.
A 'bangaren karatun Al-Qur'ani; Ash-Sheikh Albani Zaria ya fara karatun Allo ne a cikin anguwar mucciya dake Zaria. A inda ya sauke Qur'ani saukar Farko ruwayar warsh 'kira'ar Nafi'u a hannun Mallam Mato da Alarama Mallam Abubakar.
A 'bangaren Larabci kuwa Ash-Sheikh Albani Zaria ya halarci wani karatu na wata goma sha takwas (18 months) a 'karkashin wani tsarin karatu da marigayi Gaddafi ya kawo Nigeria, a 'karkashin Jagorancin jami'ar Libiya a shekara alif dubu 'daya da 'dari tara da casa'in (1990). Babban Malami, marigayi Ash-Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, shi ya dan'ka musu takardar shedar kammala karatun, kuma sai da yaba Albani Zaria wata takarda na jinjinawa ta musamman.
Dangane da sauran karatuttukan addinin musulunci kuma; Ash-Sheikh Albani Zaria yayi karatu a hannun Malamai dadama anan gida Nigeria da kuma Saudiya.
Kadan daga cikin malaman da yayi karatu a hannunsu anan gida Nigeria sunhada da; Dr. Aminuddeen Abubakar Kano (Mai makarantar Kwali), Ash-Sheikh Sani Yakubu Zaria, Shehu Umar (Malami ne a Jami'a), Alkali Mallam Haruna Ishaq Zaria. Daga bisani Ash-Sheikh Albani Zaria (Rahimahullah) ya tare a hannun wani mutumin India mai suna Dr. AbdulRahim Muhammad Muslim Khan daga Aljami'atus - Salafiyyah dake India wanda kuma malami ne dake koyarwa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria a wancan lokacin. Mallam Muhammad Muslim Khan ya karantar da Albani Zaria littattafai masu yawa. A bangaren ilimin hadisi wannan malami Muhammad Muslim Khan ya karantar da Ash-Sheikh Albani Zaria littafin tadriburra'wi da musd'alahul hadith. A bangaren sauran littattafai kuma wannan malami ya karantar da Albani littafin Sifatu-Salatin Nabiy da kuma littafin Sharhus- Sunnah na Alhafiz Al-Bagawiy(Rahimahumullaah).
Daga baya a lokacin da Ash-Sheikh Albani Zaria ya fara kasuwanci yana samun kudi, malam ya kasance yakan sayi visa da tiket na jirgi musamman dan yaje 'Kasar Saudiyya yayi karatu a matsayinshi na 'dalibi mai neman ilimi bawai a matsayinshi na 'dalibin Al - jami'atul Islamiyyah ba.
Mallam yayi karatu a gaban Dr. Muhammad Amin dake Al - jamiatul Islamiyyah dake Madina, a inda ya koyi 'kira'ar Qur'ani 'kira'a bakwai riwaya goma sha hudu.
Mallam Ya yi karatu a gaban Sheikh Uthaimin karatu sosai musamman ta fannin ilimin tafseerin Al-Qur'ani mai girma.
Mallam yayi karatun Aqeeda karatu sosai a hannun Addoktur Assihaimiy da professor Aliy Nasirul Faqihi wadanda dukkaninsu malamaine a Al - jamiatul islamiyyah dake Madina Kulliyatud-Da'awa wa usuliddeen.
Mallam yayi karatu a wurin mallam Tuwaijiri wanda ke karantarwa a Daruul-Hadeethil Khairiyyah dake Saudiyya.
Mallam yayi karatu a wajen Sheikh Zarban Al-ghamidy, wanda shi ne tsohon Bursar (shugaban 'bangaren kudi) a jami’ar Madina.
Mallam yayi karatu a hannun Sheikh Abdullahi Bn AbdulRahman Ãlu Bassãm (mai littafin Taysirul Allãm).
Mallam yayi Karatu a gaban Professor Samir wanda 'dalibi ne na Sheikh Nasiruddeenil Albaniy.
Mallam yayi karatu a hannun Muhammad ibn Aliy ibn Adam Al Ethiobiy wanda shi kuma mutumin 'kasar Ethiopia ne.
Akwai malaman jami’ar Madina dayawa wadanda malam yayi karatu a gabansu, amma ba’a matsayinshi na 'dalibi a jami’ar ba, A’a, a matsayin shi na 'dalibi wanda yakai kanshi koyon ilimi a wurinsu.
Wannan shine takaitaccen tarihin malam abinda yashafi ilimi a taqaice kwarai dagaske. Allah (SWT) muke roko da yajikan Malam ya kuma sa Aljannar Firdausi ce makomarsa.
Article Translation in English Language.
Ash-Sheikh Albani Zaria was born in the month of Rabiu Thani 1379 on 27 September 1960, in the town of Muchia in Sabon Garin Zaria in Kaduna State of Nigeria.
The teacher grew up as a child with a love of education as one of his teachers described him as saying: "Albaniy when he was young, I used to go to school; reading, where are you going; study, what are you doing; study, what have you done; apprenticeship.
His mother, Suna Saudatu, gave him the strength to study religion in particular, because she was the one who sold her goat to buy his first Saheehu Muslim book.
Also, his mother once took him when he was young and took him to some teachers in Kano town to teach him religious studies with the intention that her son would become a teacher.
In terms of reciting the Qur'an; Ash-Sheikh Albani Zaria started studying Allo in the corner of Mucciya in Zaria. In the place where he sent down the Qur'an, the first narration of the warsh 'call Nafi'u in the hands of Mallam Mato and Alarama Mallam Abubakar.
On the Arabic side, Ash-Sheikh Albani Zaria participated in a study for eighteen months (18 months) under a curriculum that the late Gaddafi brought to Nigeria, under the leadership of the University of Libya in the year one thousand nine hundred and ninety (1990).
The head teacher, the late Ash-Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, gave them the certificate of graduation, and he had to praise Albani Zaria with a special letter of appreciation.
As for other Islamic studies; Ash-Sheikh Albani Zaria studied under the right teachers here in Nigeria and Saudi Arabia.
Some of the teachers he studied under here in Nigeria include; Dr. Aminuddeen Abubakar Kano (Owner of Kwali School), Ash-Sheikh Sani Yakubu Zaria, Shehu Umar (University Teacher), Judge Mallam Haruna Ishaq Zaria. Later, Ash-Sheikh Albani Zaria (Rahimahullah) joined the hands of an Indian man named Dr. AbdulRahim Muhammad Muslim Khan from Aljami'atus - Salafiyyah in India who was a teacher at Ahmadu Bello University in Zaria at that time.
Mallam Muhammad Muslim Khan taught Albani Zaria many books. In the field of hadith knowledge, this teacher Muhammad Muslim Khan taught Ash-Sheikh Albani Zaria the book of tadriburra'wi and musd'alahul hadith.
In terms of other books, mallam taught Albani the book Sifatu-Salatin Nabiy and the book Sharhus-Sunnah by Alhafiz Al-Bagawiy (Rahimahumullaah). Later, when Ash-Sheikh Albani Zaria started a business and earning money, the teacher used to buy a visa and a plane ticket, especially if he went to Saudi Arabia to study as a student seeking knowledge, not as a student of Al-Jamiatul Islamiyyah.
Mallam studied in front of Dr. Muhammad Amin at Al - Jamiatul Islamiyyah in Madinah, where he learned to recite the Qur'an in fourteen narrations.
Mallam He studied in front of Sheikh Uthaimin very much, especially in the field of knowledge of the interpretation of the great Qur'an.
0 Comments:
Post a Comment