Sojojin Najeriya 9 ne suka mutu sakamakon tashin bom a jihar Borno

Sojojin Najeriya 9 ne suka mutu sakamakon tashin bom a jihar Borno

Sojojin Najeriya 9 ne suka mutu sakamakon tashin bom da Kungiyar Boko Haram ta binne akan hanya, a jihar Borno.

Akalla sojojin Najeriya tara ne suka mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata, a lokacin da ayarin motocinsu suka taka wata nakiya da aka binne, sannan kuma suka yi musu luguden wuta a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, kamar yadda wasu majiyoyin tsaro biyu suka bayyana a ranar Litinin.

An kai harin ne a ranar Lahadi a kusa da kauyen Bindundul mai tazarar kilomita 20 daga Kareto.

“Yan ta’addan sun dasa nakiyar da sojojinmu suka taka, abin takaicin shi ne, sojoji kusan tara ne suka mutu nan take, yayin da wasu biyar suka samu munanan raunuka,” in ji Abba Kaka Tuja, wani mamba na rundunar hadin gwiwa ta Civilian Task Force da ke aikin ceto.



SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: