Yara 5 ne suka mutu sakamakon ruftawar katanga a jihar Borno.

Yara 5 ne suka mutu sakamakon ruftawar katanga a jihar Borno.

.

Ya ce, “Al’amarin ya faru ne a ranar Lahadi da misalin karfe 8:00 na dare, mun samu rahoto ta hannun jami’in ‘yan sanda reshen Bulumkutu cewa katanga ta ruguje ne akan yara shida.”

“Abin takaici, biyar daga cikin yaran, wadanda ‘yan kasa da shekaru 16, sun rasa rayukansu, yayin da daya ya samu raunuka kuma a halin yanzu yana jinya a asibiti.”

Ya ce ana ci gaba da kokarin gano musabbabin faruwar lamarin.

Daso ya kuma yi kira ga jama’a da su tabbatar da tsarin da ya dace wajen gine-gine da kuma sanya ido sosai kan yara.

Ya kara da cewa "Muna kira ga jama'a da su kula da tsarin, kiyaye ka'idojin gini, da kuma sanya ido sosai kan 'ya'yansu."


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: