Shugabar rikon kwaryar Venuzuela, Delcy Rodriguez ta ce a shirye take ta hada kai da Amurka kan makomar kasar

Shugabar rikon kwaryar Venuzuela, Delcy Rodriguez ta ce a shirye take ta hada kai da Amurka kan makomar kasar

Shugabar rikon kwaryar Venuzuela, Delcy Rodriguez ta ce a shirye take ta hada kai da Amurka kan makomar kasar, a wani gagarumin sauyi da ya biyo bayan farmakin da ya kai ga sace shugaba Nicolas Maduro da dakarun Amurka na musamman suka yi.

"Muna la'akari da shi a matsayin fifiko don matsawa zuwa daidaito da dangantaka mai mutuntawa tsakanin Amurka da Venezuela," Rodriguez ya rubuta a kan Telegram ranar Lahadi.

Kalaman na ta yazo ne sa'o'i kadan bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya shaidawa manema labarai cewa, Amurka a shirye take ta kai harin soji na biyu a kan kasar Venezuela idan gwamnatinta ta ki ba da hadin kai da shirinsa na ‘yantar da halin da Venuzuela ke ciki, bayan sace shugaba Nicolas Maduro da Amurkan ta yi.

Ta ci gaba da cewa, 
"Muna mika goron gayyata ga gwamnatin Amurka don yin aiki tare a kan wani ajanda na hadin gwiwa da ke da nufin samun ci gaba tare."

Rodriguez, wanda ta rike mukamin mataimakin Maduro tun shekarar 2018, kotun kolin Venezuela ta nada ta shugaban rikon kwarya a ranar Asabar bayan da aka tsare Maduro da matarsa, Cilia Flores a hari mafi girma da hadari na sojojin Amurka su taba aiwatarwa tun bayan da rundunar sojin ruwa ta Amurka SEAL ta kashe shugaban al-Qaeda Osama bin Laden a wani gida mai tsaro a Abbottabad na Pakistan a 2011.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: