Rade-radin cewa Amurka ta yi kokarin kashe ni a lokacin harin da ta kawo Najeriya, Ba gaskiya ba ne, - Sheikh Ahmad Mahmud Gumi.

Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ya musanta ikirarin cewa Amurka ta Kai hari domin ta kashe shi ne

Rade-radin cewa Amurka ta yi kokarin kashe ni a lokacin harin da ta kawo Najeriya, Ba gaskiya ba ne, - Sheikh Ahmad Mahmud Gumi.

Babban Malamin addinin Musulunci da ke zaune a Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya musanta ikirarin da ake yadawan cewa, ya samu labarin cewa, Amurka ta yi kokarin kawar da shi, a harin da ta kai ta sama kan 'yan ta'adda a jihar Sokoto.

Gumi ya ce rahotannin sun samo asali ne daga wani tsohon faifan bidiyo da a baya ya yi magana game da barazanar da ake yi wa rayuwarsa, inda ya kara da cewa ya yi wadannan kalamai ne dangane da rikicin Boko Haram.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, malamin ya bayyana cewa wasu ‘yan kungiyar Boko Haram da ake zargin sun yi yunkurin kashe shi a shekarar 2012, yana mai jaddada cewa lamarin ba shi da alaka da harin da Amurka ta kai a baya-bayan nan.

Ya kara da cewa a halin yanzu rayuwarsa ba ta cikin hadari kuma babu wata barazana da ke tattare da tsaron lafiyarsa sabanin ikirarin da ke yawo a shafukan sada zumunta.

Gumi ya ce da yardar Allah ya tsallake rijiya da baya a yunkurin kashe shi da aka yi, inda ya ce wadanda suka aikata wannan aika-aika suna gudanar da ayyukansu ne da sunan Boko Haram.

Ya rubuta cewa, “Akwai labaran karya da ke yaduwa a yanzu da ke ikirarin cewa na ce harin da Amurka ta kai a Najeriya, ta kai ne domin ta kashe ni.

“Ban taɓa cewa haka ba, kuma ban taɓa tunanin irin wannan yuwuwar ba, Ina zama cikin kwanciyar hankali a gidana tare da iyalina ba tare da tsoro, ko fargaba ba.

“Na yi imanin cewa tushen fassara shi ne lacca da na yi a masallacin kan yadda, a watan Agustan 2012, aka gaya mini cewa Boko Haram ta kai wani hari don ta kawar da ni.

“Mutane biyu da suka zo aiwatar da shirin an kashe su nan take lokacin da bam din ya tashi a hannunsu a kusa da gidana.

"Ina ba da shawara ga duk kamfanonin dillancin labarai da suka ruwaito labarin na karya da su janye shi a bainar jama'a tare da bayar da hakuri."


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: