Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da harin da aka kai a kasuwar jihar Neja, tare da nuna alhininsu kan iftala'in hadarin kwale-kwale a jihar Yobe.
Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa, ta yi Allah wadai da kakkausar murya dangane da harin ta’addancin da aka kai a Kasuwar Daji da ke cikin unguwar Demo a karamar hukumar Borgu ta Jihar Neja, inda ta bayyana hakan a matsayin babban cin zarafi ga ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba, kuma babbar barazana ce ga zaman lafiya da rayuwa.
Rahotanni sun ce an kashe ‘yan kasuwa a kalla 30 da suka hada da mata da maza, tare da sace wasu da dama, sannan kasuwar ta kone kurmus a harin da wasu da ake zargin ‘yan ta’addan daji ne suka kai.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a madadin takwarorinsa, Shugaban kungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya, Daraktan Yada Labarai na Gidan Gwamnatin Gombe Ismaila Misilli ne ya aike da sanarwar, ya bayyana matukar kaduwa da bacin rai game da lamarin, tare da nuna rashin jin dadinsa ga iyalai, da kawo cikas ga harkokin tattalin arziki da kuma rashin zaman lafiya a tsakanin al’umma.
Yahaya ya jaddada cewa irin wannan ta'addancin da ake yi wa 'yan kasuwa da 'yan kasa da ke gudanar da ayyukansu na halal abin zargi ne da kuma cin zarafin jama'a da tattalin arzikin yanki.

0 Comments:
Post a Comment