‘Yan jaridu 128 aka kashe a shekarar 2025 - IFJ

‘Yan jaridu 128 aka kashe a shekarar 2025 - IFJ

‘Yan jaridu 128 aka kashe a shekarar 2025 da ta gabata, fiye da rabinsu a yankin gabas ta tsakiya, in ji kungiyar ‘yan jaridu ta duniya (IFJ).

Kungiyar ta bayyana fargaban ta musamman kan halin da ake ciki a yankunan Falasdinawa, inda ta ce an kashe kwararrun 'yan jaridu 56 a shekarar 2025 a yakin da Isra'ila ta yi da Hamas a Gaza.

Babban sakatare na kungiyar ta IFJ Anthony Bellanger ya shaida wa AFP cewa,

"Ba mu taba ganin wani abu makamancin haka ba: mace-mace da yawa a cikin kankanin lokaci, a irin wannan karamin yanki," in ji Bellanger.

An kuma kashe ‘yan jaridu a kasashen Yemen da Ukraine da Sudan da Peru da India da sauran wurare.

Bellanger ya yi Allah wadai da abin da ya kira "rashin hukunci" ga wadanda suke kai hari kan 'yan jaridun. 

"Idan ba a daukar hukunci da adalci, yana ba da damar masu kashe 'yan jarida su ci gaba," in ji shi.


A halin da ake ciki, IFJ ta ce a fadin duniya ‘yan jaridu 533 ne ke tsare a gidan yari -- adadin da ya ninka fiye da rabin na shekarun da suka gabata.

Kasar Sin ta sake zama kan gaba a jerin sunayen Kasashen da Kungiyar ta ce suna take hakkin 'yan jaridu, inda ta daure 'yan jaridu 143 a gidan yari, ciki har da Hong Kong, inda mahukuntan kasashen yammacin duniya ke sukar hukumomin kasar kan sanya dokar  da ke murkushe 'yan adawa.

Alkaluman kididdigar da IFJ ta yi na yawan ‘yan jaridan da aka kashe ya zarce na kungiyar Reporters Without Borders, saboda hanyoyin kidaya daban-daban. 

Adadin wadanda suka mutu a shekarar a Rahotan na IFJ harda mutane tara da suka mutu ta hanyar hadari.

A nata kididdigar, Kungiyar Reporters Without Borders ta ce an kashe ‘yan jarida 67 a cikin aikinsu a bana, yayin da UNESCO ta ce adadin ya kai 93.



SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: