Akalla ‘yan Najeriya 141 ne aka kama a Ghana bisa zarginsu da hannu a laifukan hada-hadar kudi ta yanar gizo da suka hada da damfara ta wayar salula da kuma damfara ta email na kasuwanci.
Kamen dai ya biyo bayan wani shirin hadin gwiwa ne da hukumar tsaro ta yanar gizo ta Kasar Ghana tare da hadin gwiwar hukumar 'yan sandan Ghana da tsaron kasa da kuma hukumar shige da fice ta Ghana suka gudanar.
A cewar wata sanarwa da kwamishinan sadarwa da fasahar dijital da kere-kere na Ghana, Samuel George ya fitar ranar Asabar, an gudanar da samamen ne a wasu muhimman wurare a Tabora da Lashibi.
Sanarwar ta bayyana cewa an kama mutane 100 da ake zargin ne a Tabora, yayin da aka kama wasu 41 a garin Lashibi, wanda ya kawo adadin wadanda aka kama zuwa 141.
Binciken farko ya nuna cewa wadanda ake zargin ‘yan Najeriya ne.
Hukumomin tsaro sun kuma gano kwamfutoci 38 da wayoyin hannu 150 da ake zargin an yi amfani da su wajen aikata laifukan hada-hadar kudi ta yanar gizo.
A yayin aikin, an kuma kama wani mai bayar da hayan gida dan kasar Ghana wanda ake zargin ya ajiye masu laifin kusan su 100 a gidansa.
Hukumomin sun yi gargadin cewa masu gidaje suna da alhakin tabbatar da cewa ba a yi amfani da kadarorin su ba don sauƙaƙe ayyukan aikata laifuka.
Ana zargin wadanda ake zargin da hannu a laifukan da suka hada da damfara ta wayar salula, damfarar soyayya, damfaran kasuwanci ta Email da kuma zamba ta waya.
Sanarwar ta ce "ana ci gaba da gudanar da bincike kan na'urorin da aka kama, kuma mutanen da aka samu da laifi za a hukunta su kamar yadda dokar Kasar Ghana ta tanada."
Hukumomin Ghana sun bukaci jama'a da su yi taka tsantsan tare da bayar da rahoton abubuwan da ake zargi na fasahar yanar gizo, tare da jaddada aniyar kasar na yakar laifukan yanar gizo.
Sanarwar ta kara da cewa, "Ghana na ci gaba da maraba da dukkan abokai da makwabta masu sha'awar kasuwanci ta halal, amma idan kuna sha'awar aikata laifuka ta yanar gizo, za mu same ku, mu kama ku, kuma za mu yi maganin ku bisa ga dokokinmu."

0 Comments:
Post a Comment