An sake kashe mutum uku, tare da yin garkuwa da wasu mutum uku a harin da ‘yan bindiga su ka kai jihar Kaduna.
Akalla mutane uku ne aka kashe yayin da wasu 3 aka yi garkuwa da su bayan wani hari ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne suka kai cikin dare a kauyen Bundu Kahugu da ke karamar hukumar Lere a jihar Kaduna.
Harin wanda rahotanni suka ce ya faru ne da misalin karfe 11 na daren ranar Litinin, 29 ga watan Disamba, 2025, ya jefa al’umman garin cikin alhini tare da sake kiraye-kirayen inganta harkokin tsaro a yankin.
Sakataren al’ummar Bundu Kahugu, Ishaya Dauda, wanda ya tabbatar wa da manema labarai faruwar lamarin a yau Talata, ya ce maharan sun mamaye kauyen ne a cikin duhu, inda suka yi ta harbe-harbe tare da tsoratar da mazauna kauyen.
A cewarsa, makwanni biyu kacal da suka gabata ne al’ummar yankin suka fuskanci irin wannan hari, inda aka kashe mutane hudu, lamarin da ya kara nuna damuwa kan hare-haren da ake kaiwa yankin.
“Maharan sun zo ne cikin daddare, inda suka fara harbe-harbe, nan take su ka kashe mutane uku, yayin da su ka tafi da wasu uku, wannan shi ne karo na biyu da aka kai wa al’ummarmu hari cikin ƙasa da makonni biyu,” inji shi.
Wadanda aka kashe a harin na baya-bayan nan sun hada da Felix Augustine, Luka Yakubu da Ezra Namata.
Mazauna yankin sun yi kira ga gwamnatin jihar Kaduna da jami’an tsaro da su gaggauta tura jami’an soji yankin domin dakile ci gaba da kai hare-hare.
Sun kuma yi kira ga kamfanonin sadarwa da su inganta hanyoyin sadarwa a kauyakun, Saboda maharan sukan yi amfani ne da rashin ingancin hanyoyin sadarwa ne wajen kai hare-haren su cikin walwala da kuma tserewa ba tare da turjiya ba.
"Don haka Muna rokon gwamnati da ta taimaka mana wajen gyara hanyoyin sadarwa donin hana taimaka wa maharan, muna bukatar samar da tsaro da ingantattun hanyoyin sadarwa domin ceto mutanenmu," in ji shugaban al'ummar.
Kokarin jin martani daga rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna har zuwa lokacin hada wannan rahoto ya ci tura.
Source: Punchng

0 Comments:
Post a Comment