Shugaban Majalisar Wakilai, Dr Tajudeen Abbas, ya yi Allah-wadai da tashin bam a jihar Zamfara da ya yi sanadin mutuwar mutane bakwai.
Lamarin ya faru ne a ranar Asabar din da ta gabata lokacin da wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka dasa bam a kan babbar hanyar Magami zuwa Dansadau a karamar hukumar Maru.
Bom din ya fashe ne yayin da wata motar bas da ke dauke da fasinjoji ta bi ta kai, inda nan take ya kashe mutane bakwai.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata ta hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Musa Krishi, shugaban majalisar ya bayyana harin a matsayin na matsorata da rashin tausayi.
A cewarsa, “Abin takaici ne yadda aka kai harin jim kadan bayan da gwamnatocin Najeriya da na Amurka suka kaddamar da farmakin hadin gwiwa na yaki da ta’addanci a kasar, tare da kai hare-hare a maboyar ‘yan ta’adda a sassan Arewa maso Yamma a ranar Alhamis.”
Abbas ya ce Gwamnatin Tarayya ta bullo da sabbin tsare-tsare na tsaro don duba ayyukan ta’addanci, yana mai jaddada cewa za a ci gaba da dakile ayyukan ta’addanci, ‘yan fashi da sauran laifukan da ake yi wa jihar.
Ya kara da cewa ‘yan Najeriya sun kuduri aniyar marawa gwamnatin shugaba Bola Tinubu baya a yunkurinta na magance barazanar rayuwa da dukiyoyi a fadin kasar nan.
Abbas ya ce Gwamnatin Tarayya ta bullo da sabbin tsare-tsare na tsaro don duba ayyukan ta’addanci, yana mai jaddada cewa za a ci gaba da dakile ayyukan ta’addanci da na ‘yan fashi da sauran laifukan da ake yi a jihar.
Ya kara da cewa ‘yan Najeriya sun kuduri aniyar marawa gwamnatin shugaba Bola Tinubu baya a yunkurinta na magance barazanar rayuwa da dukiyoyi a fadin kasar nan.
Shugaban majalisar ya kuma yi alkawarin shirin majalisar na samar da tallafin da ya dace na majalisa da kasafin kudi domin tunkarar kalubalen tsaron kasar.

0 Comments:
Post a Comment