Jam'iyar NNPP a Kano zata maye gurbin takaran kujerun 'yan majalisar dokokin jihar da su ka rasu da 'ya'yayensu.

Jam'iyar NNPP a Kano zata maye gurbin takaran kujerun 'yan majalisar dokokin jihar da su ka rasu da 'ya'yayensu.

Jam'iyar NNPP a Kano zata maye gurbin takaran kujerun 'yan majalisar dokokin jihar da su ka rasu da 'ya'yayensu.

Jam’iyyar  (NNPP) a jihar Kano ta ce ta samu fahimtar juna da iyalan ‘yan majalisar dokokin jihar Kano biyu da suka rasu kan yadda za a maye gurbin mamatan da 'ya'yayen na su.

Da yake magana a wata hira da DCL Hausa, shugaban jam’iyyar na jihar, Dokta Hashim Sulaiman Dungurawa, ya ce yarjejeniyar ta biyo bayan shawarwari da dama da Jagoran jam’iyyar na kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya jagoranta

A cewar Dungurawa, Kwankwaso ya gana da manyan shugabannin jam’iyyar da kuma ‘yan uwan wadanda suka rasu a gidansa da ke Kano, inda suka tattauna yadda za a maye gurbinsu.

"Akwai fahimta da girmamawa a kowane bangare. Mun zauna, mun yi magana a zahiri, kuma mun amince da tsarin," in ji Dungurawa

Ya yi nuni da cewa jam’iyyar na fatan Sa’ad Aminu Sa’ad da Nabil Aliyu Daneji da ake ganin za su maye gurbinsu, za su yi aiki daidai da ka’ida da aikin gwamnati irin na  mahaifansu

Ya kara da cewa "Mun yi imanin za su ci gaba da yin hidima da sadaukar da kai da aka san mahaifansu da shi."

‘Yan majalisar biyu sun rasu ne a ranar 24 ga watan Disamba, 2025, bayan sun yi fama da ciyo a tsaitsaye, inda suka bar gibi a majalisar dokokin jihar ta Kano.

Dungurawa ya jaddada cewa, jam’iyyar NNPP ta dukufa wajen gudanar da aikin maye gurbin cikin lumana, da mutuntawa, da kuma bin doka, inda ya kara da cewa, dukkan matakai za su bi ka’idojin jam’iyya da ka’idojin zabe.



SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: