Akalla mutane takwas ne suka mutu sannan wasu fiye da 18 suka jikkata a wani harin bam da aka kai a wani masallaci a lardin Homs na kasar Syria, a cewar jami’an yankin.
Kamfanin dillancin labaran Syria SANA ya habarta cewa, an kai harin ne a masallacin Imam Ali bin Abi Talib da ke unguwar Wadi al-Dahab a birnin Homs a lokacin sallar Juma'a.
Hotunan da gidan talabijin na Aljazeera ya tabbatar ya nuna yadda mutanen suka tsere daga masallacin cikin firgici, inda suka ajiye wasu da abin ya rutsa da su a kan shimfida, sannan dauke da wasu, nannade da mayafi, zuwa motocin daukar marasa lafiya.
Ga dukkan alamu fashewar ta auku ne a kusurwar babban dakin ibada na masallacin, inda wani dan karamin sako a bangon ya kone, tare da shinfidan sallah da tarkace, da litattafai duk sun watse a kasa.
Jami’an yankin sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa fashewar ta yiwu wani dan kunar bakin wake ne ko kuma bama-bamai da aka ajiye a wurin.
Ma'aikatar harkokin cikin gidan Syria ta ce jami'an tsaron sun sanya shinge a kusa da yankin kuma suna gudanar da bincike.
Ayman Oghanna, wakilin Al Jazeera a Aleppo, ya lura cewa Homs gida ne ga al'ummar Alawites, Kiristanci da kuma Musulmi 'yan Sunni.
Ya ce harin da aka kai masallacin zai iya "rura wutar rikicin addini" a fadin kasar.
Ya ce babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin a yanzu, sai dai ya yi nuni da cewa a baya-bayan nan ana samun karuwar ayyukan kungiyar ISIL a Syria.
Ya kara da cewa dakarun gwamnati sun kai wani samame a kusa da birnin Aleppo, inda suka kama mutane uku da ake zargin 'yan ISIL ne.

0 Comments:
Post a Comment