Kwankwaso ya karbi bakuncin talibai 300 da su ka kammala Karatun digirin digirgir, PhD karkashin shirin tallafin karatu na Kwankwasiyya.
Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya karbi bakuncin dalibai 300 da suka samu digirin digirgir (PhD) da aka samar ta hanyar shirin tallafin karatu na Kwankwasiyya a babban taron shekara-shekara na Kwankwasiyya da aka gudanar a Kano.
Kwankwaso ya bayyana ilimi a matsayin gado mafi dawwama da kowane shugaba zai bari a baya, yana mai jaddada cewa dorewar zuba jari domin tasiri ga rayuwar dan Adam shine ainihin ma’aunin shugabanci na gari.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar malaman Kwankwasiyya ta kasa, Dakta Mansur Hassan, kuma aka rabawa manema labarai a Kaduna ranar Alhamis.
Da yake jawabi a wajen taron wanda ya hada wadanda suka ci gajiyar shirin tallafin karatu na tsawon shekaru kusan 25, Kwankwaso ya bayyana taron a matsayin mai tarihi ga jihar Kano da Najeriya baki daya.
"Na tuna da yawa daga cikinku lokacin da kuke ƙarami, wasunku kamar kun fito ne kai tsaye daga ƙauyuka, a yau, ina ganin ƙarfin gwiwa da ƙwarewa a tattare da ku ," in ji shi.
Ya kara da cewa taron ya nuna muhimmancin jagoranci, dorewa da kuma hangen nesa, inda ya kara da cewa kamata ya yi a yi la’akari da yadda tsarin mulki ya dade yana tasiri ga rayuwar ‘yan kasa.
Kwankwaso ya bayyana cewa bayan zaben 2019 da gwamnati ta daina daukar nauyin daliban kasashen waje, ya yanke shawarar ci gaba da gudanar da shirin ta hanyar gidauniyar Kwankwasiyya Development Foundation.

0 Comments:
Post a Comment