Firayim Ministan Israi'la, Benjamin Netanyahu ya sanar a yau litinin cewa, Isra'ila ba za ta kyale babbar abokiyar gabarta, Iran ta dawo da shirinta na makami mai linzami ba, kwanaki kadan bayan shugaban Amurka Donald Trump ya yi irin wannan barazanar.
"Ba za mu bar Iran ta dawo da masana'antarta ta makamai masu linzami ba, kuma tabbas ba za mu bari ta sabunta shirin nukiliyar da muka lalata ba," Netanyahu, Lokacin davyake jawabi ga 'yan majalisar ƙasar.
"Idan aka kai mana hari, sakamakon da Iran za ta fuskanta zai yi tsanani," in ji shi.
Barazanar Netanyahu na zuwa ne kwanaki kadan bayan Trump ya yi barazanar "kawar da" shirin nukiliyar Iran da makami mai linzami, bayan da shugabannin biyu suka gana a Washington a makon jiya.
Jami’ai da kafafen yada labaran Isra’ila sun bayyana damuwarsu a ‘yan watannin nan cewa Iran na sake kera makamanta na makami mai linzami bayan ta lalace a yakin kwanaki 12 da Isra’ila ta yi a watan Yuni.
Trump ya ce Iran tana iya yin mugun hali, kuma tana duba sabbin wuraren nukiliyar da za ta maye gurbin wadanda hare-haren da Amurka ta kai a lokacin rikici, tare da maido da makamanta masu linzami.
"Ina fatan ba za su sake yin farfado da shirin ba saboda idan sun cigaba, ba mu da wani zabi face da sauri don kawar da wannan ginin," in ji Trump, yana mai kara cewa martanin Amurka "na iya zama mafi karfi fiye da na baya."
Amma Trump ya ce ya yi imani har yanzu Iran na sha'awar kulla yarjejeniya da Amurka kan shirinta na nukiliya da makamai masu linzami.
Sai dai Iran ta sha musanta cewa tana neman kera makaman nukiliya.
Netanyahu, ya ce zanga-zangar da aka yi a Iran ta "kara fadada sosai".
"Akwai yiwuwar mu kasance a wani muhimmin lokaci - lokacin da al'ummar Iran za su dauki makomarsu a hannunsu," in ji shi a cikin majalisar.
Zanga-zangar ta barke a Iran ne a ranar 28 ga watan Disamba lokacin da masu shaguna a Tehran babban birnin kasar suka gudanar da yajin aikin saboda tsadar kayayyaki da tabarbarewar tattalin arziki.
Tun daga nan suka bazu zuwa wasu garuruwa kuma suka fadada har da buƙatun siyasa.
Netanyahu ya Kara da cewa, Isra'ila za ta tsaya tsayin daka da al'ummar Iran a yayin zanga-zangar da ake yi.
"Muna goyon bayan gwagwarmayar al'ummar Iran da kuma burinsu na samun 'yanci da adalci."

0 Comments:
Post a Comment