Tsohon Gwamnan jhar Zamfara Kuma Karamin ministan tsaron Najeriya, Bello Matawalle zai aurar da ’ya’yansa maza da mata guda tara a Abuja.
A cikin Katin gayyatar daurin auren wanda ya yadu a shafukan sada zumunta, an bayya cewa za'a gudanar da bikin daurin auren ne a ranar Asabar da karfe 1:30 na rana ranar 6 ga watan Fabrairu, a babban masallacin Abuja.
Sunayen yaran sune: Ibrahim, Suraj, Safiya, Maryam, Aisha, Fahad, Muh’d, Nana Firdausi, da Farida.

0 Comments:
Post a Comment