Jami'an tsaro sun fara farautar wadanda suka kashe wata mata da 'ya'yanta shida a jihar Kano.

Jami'an tsaro sun fara farautar wadanda suka kashe wata mata da 'ya'yanta shida a jihar Kano.

Jami'an tsaro sun fara farautar wadanda suka kashe wata mata da 'ya'yanta shida a jihar Kano.

Wata mata da ‘ya’yanta shida sun mutu a wani mummunan kisa da aka yi musu a gidansu da ke unguwar Dorayi Chiranchi Quarters a jihar Kano.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Abdullahi Haruna ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.

A cewar sanarwar, an kai harin ne da sanyin safiyar ranar 17 ga watan Janairun 2025, lokacin da wasu da ba a san ko su wanene ba suka shiga gidan wadanda abin ya shafa da karfi.

An baiyana wanda aka kashen da suna Fatima Abubakar mai shekaru 35 da ‘ya’yanta shida. 
Rahotannin farko ya nuni cewa sun samu munanan raunuka yayin harin.

Da samun rahoton kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Ibrahim Bakori, ya tara tawagar jami’an tsaro zuwa wurin, karkashin jagorancin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da ayyuka, Lawal Mani.

Tuni dai rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta fara gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin tare da cafke wadanda ke da hannu a lamarin.


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: