Hukumomin Jami'ar Bayero (BUK) dake Kano sun kori dalibai 60 saboda samun su da laifin satar amsa a lokacin jarabawa.
An dauki matakin ne a taron majalisar dattijai na jami’ar karo na 43, bayan nazarin rahotanni da shawarwarin da kwamitocin ilimi da ladabtarwa suka gabatar.
An sanar da korar daliban ne a cikin jaridar 'Weekly Bulletin' na jami’ar da aka buga a ranar Juma’a, inda ta bayyana cewa an samu daliban da da laifin karya ka’idojin jarrabawar jami’ar.
Sanarwar ta kara da cewa, "Bayan nazarin shari'ar, majalisar dattijai ta amince da korar daliban kamar yadda ka'idar jarrabawar jami'ar ta tanada."

0 Comments:
Post a Comment