Mahaifin wanda ake zargi da kashe wata mata da 'ya'yanta shida a jihar Kano ya bukaci Gwamnati ta gaggauta kashe dansa

Mahaifin wanda ake zargi da kashe wata mata da 'ya'yanta shida a jihar Kano ya bukaci Gwamnati ta gaggauta kashe dansa.

Mahaifin wanda ake zargi da kashe wata mata da 'ya'yanta shida a jihar Kano ya bukaci Gwamnati ta gaggauta kashe dansa.

Mallam Awal, mahaifin wanda ake zargi da laifin Jagorantar kisan gillar da aka yi wa wata mata da ‘ya’yanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi da ke cikin birnin Kano, ya yi kira ga gwamnati da ta gaggauta kashe dansa, ba tare da tsare shi a gidan yari ba.

Ranar 17 ga wannan watan ne Al'ummar unguwar Dorayi Chiranci suka shiga cikin yanayi na iftala'in Kisan gilla wanda aka yi ma wata mata da'yayanta su shida a cikin gidansu.
Lamarin dai ya tayar da hankalin Al'ummar unguwar Dorayi Chiranci da sauran sassan Najeriya.
Bayan gudanar da bincike ne, jami'an tsaron jihar Kano suka sanar da kama mutum uku da ake zargi da aikata wannan kisan rashin Imani, Wanda Umar da ga Malam Auwal ya Jagoranci abokan nasa domin gudanar da wannan danyan aiki.
Mahaifin ya baiyana wacce aka kashe a matsayin kanwarsa, Ma'ana guggon Umar kenan wanda ya Jagoranci kisan.

Saurari Cikakken firan da aka yi da shi a kasa.👇🏽


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: