Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta yi nasaran kama wadanda su ka kashe wata mata da 'ya'yanta shida a jihar


Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke wasu mutane uku da ake zargi da kashe wata mata da ‘ya’yanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi da ke birnin Kano.

Kamen dai ya biyo bayan umarnin babban sufeton ‘yan sanda Kayode Egbetokun ne, karkashin jagorancin kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Ibrahim Bakori.

A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, Abdullahi Kiyawa ya fitar a yau Lahadi, ya bayyana wadanda ake zargin Umar Auwalu mai shekaru 23; Isyaku Yakubu (wanda aka fi sani da Chebe), mai shekaru 40 da Yakubu Abdulaziz (wanda aka fi sani da Wawo) mai shekaru 21.

An kama mutanen uku ne a wani samame da aka yi daga karfe 10 na daren ranar Asabar zuwa karfe hudu na asubahin yau Lahadi.

Kiyawa ya ce bincike ya gano cewa Auwalu, dan uwa ga matar marigayin, shi ne jagoran lamarin kuma ya amsa laifinsa.

Kakakin ya ce, Auwalu ya amsa cewa sun aiwatar da kashe-kashe a baya, wandada suka hada da kisan kai da kona wasu mata biyu a Tudun Yola Quarters a Kano.

Kiyawa ya ce, kayayyakin da aka kwato a hannun makisan sun hada da tufafi hudu masu dauke da jini, wayoyin hannu guda biyu na wadanda aka kashe da kulake (wanda aka fi sani da gora), da wasu kudade, da sauran muggan makamai.

Rundunar ‘yan sandan ta yaba wa jami’an ta bisa gaggawa da suka yi, sannan ta gode wa jama’a bisa hadin kai da goyon bayan da suka ba su, tare da tabbatar wa mazauna jihar ci gaba da kokarin tabbatar da adalci da dorewar zaman lafiya a jihar, yayin da ake ci gaba da bincike.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: