An samu fashewar Bam a wani gidan cin abinci na 'yan ƙasar Sin da ke babban birnin kasar Afganistan, Kabul, inda ya kashe wani dan ƙasar Sin da kuma 'yan kasar Afghanistan su shida tare da jikkata wasu da dama ciki har da wani yaro, kamar yadda jami'an ƙasar suka sanar.
Gidan abincin da fashewar ta afku a jiya Litinin yana a unguwar kasuwanci ne ta Shahr-e-Naw da ke birnin Kabul wanda ya hada da gine-ginen ofisoshi, shaguna da ofisoshin jakadanci, in ji kakakin 'yan sanda Khalid Zadran.
Ana ɗaukar gundumar ɗaya daga cikin wurare mafi aminci da zaman lafiya a cikin birni.
Zadran ya ce, wani musulmi dan ƙasar Sin, Abdul Majid, da matarsa, da wani abokin aikin sa, Abdul Jabbar Mahmood, ne ke gudanar da gidan cin abinci na 'yan ƙasar Sin tare.
Ya kara da cewa, wani dan kasar Sin mai suna Ayub, da kuma 'yan kasar Afghanistan shida ne suka mutu sakamakon fashewar bam din da ya afku a kusa da kicin, yayin da wasu da dama suka jikkata.
Kungiyar ISIL reshen Afganistan daga baya ta dauki alhakin harin na ranar Litinin, inda ta ce wani dan kunar bakin wake ne ya kai harin.
Kamfanin dillancin labaran Amaq na ISIL ya ce kungiyar ta sanya 'yan ƙasar Sin a cikin jerin sunayen wadanda ta ke kai wa hari, inda ta yi nuni da "laifi da yawa da gwamnatin ƙasar Sin ke yi kan musulmi 'yan kabilar Uighur".

0 Comments:
Post a Comment