Adadin wadanda suka mutu sakamakon gobara da ta tashi a wata cibiyar kasuwanci a birnin Karachi a karshen mako ya kai akalla 14, a cewar hukumomin Pakistan, yayin da ake ci gaba da neman mutane sama da 50 da suka bata.
Mataimakin babban sufeton ‘yan sandan Kudu, Syed Asad Raza, ya shaidawa jaridar Dawn a yau Litinin cewa, jami’an ceto sun sake gano wasu gawarwaki takwas tun da yammacin ranar Lahadi, wanda ya kai adadin wadanda suka mutu daga shida zuwa 14.

0 Comments:
Post a Comment