Tinubu ya gana da shuwagabannin Sojoji da na 'yan sanda a Abuja.

Tinubu ya gana da shuwagabannin Sojoji da na 'yan sanda a Abuja.

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi wata ganawar tsaro da hafsoshin tsaro a Abuja, domin magance matsalar rashin tsaro da al’ummar kasar ke fama da su, tare da daidaita matakan da suka dace....

A jiya Lahadin ne shugaban kasa, Bola Tinubu, yayi wata ganawar tsaro da shugabannin ma’aikatan tsaron kasar a fadar gwamnati da ke Abuja.

Taron ya samu halartar babban hafsan sojin kasar, Manjo Janar Waidi Shaibu; Babban Hafsan Sojan Sama, Air Marshal Sunday Aneke; Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun; da Darakta-Janar na Ma’aikatar Ayyuka ta kasa, Tosin Ajayi.

Ganawar ta zo ne sa’o’i kadan bayan da Shugaban kasar ya jaddada aniyar gwamnatinsa na tunkarar kalubalen tsaron da kasar ke fuskanta, inda ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai an tabbatar da tsaro a kasar.

A baya dai Tinubu ya sanar da kubutar da wasu masu ibada 38 da aka yi garkuwa da su a garin Eruku na jihar Kwara da dalibai 51 da aka yi garkuwa da su a makarantar Katolika da ke jihar Neja. Ya kuma bayyana cewa ya soke tafiyarsa zuwa taron kolin G20 a Afirka ta Kudu don daidaita matakan tsaro da kansa.


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: