A wasannin da aka buga a jiya asabar a cigaba da wasannin premier league kungiyoyi 14 ne suka fafata da juna a wasanni 7 da aka buga.
Burnley da Chelsea, inda Chelsea ta yi nasaran doke Burnley din da ci 2-0, Wanda hakan ya bata daman komawa mataki na biyu a teburin na premier league.
Sai wasa tsakanin AFC Bournemouth da West Ham United inda aka tashi wasan canjaras 2-2.
Sai Wasan Brighton da Brentford inda Brighton din ta yi nasara da ci 2-1.
Sai Fulham wacce ta doke Sunderland da ci da ya mai ban haushi.
Sai Nottingham Forrest wacce ta bi Liverpool din har filin wasa na Anfield ta lallasa ta da ci 3-0.
Haka zalika ita ma Crystal Palace ta bi Wolverhampton har gida inda ta doke ta da ci 2-0.
Sai Newcastle United wacce ta doke Manchester City da ci 2-1 a filin wasanta na Godison Park.
Sauran wasannin da za'a buga a yau sune tsakanin.
Leeds United da Aston Villa
Arsenal da Tottenham hostpur
Sai gobe litinin tsakanin Kungiyar kwallon kafar
Manchester United da Everton

0 Comments:
Post a Comment