Allah yayi wa Shahararren malamin addinin musulunci kuma Jagoran Darikar Tijjaniya a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi rasuwa yana da shekaru 101 a duniya.

Allah yayi wa Shahararren malamin addinin musulunci kuma Jagoran Darikar Tijjaniya a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi rasuwa yana da shekaru 101 a duniya.

Inna Lillahi wa inna ilaihi raji'un.

Shahararren malamin addinin musulunci kuma Jagoran Darikar Tijjaniya a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya rasu yana da shekaru 101 a duniya.

Sheikh Dahiru Bauchi ya rasu ne a daren jiya laraba 5 Jumada Akhir, 1447 daidai da 25 Nuwanba, 2025 yana da shekaru 101 a duniya a kirgan kwanakin hijra, yayin da yake da Shekaru 98 a kirgan kwanakin Miladiya na haihuwuwar Annabi Isah (AS).

Majiyoyin da muka samu sun tabbatar da cewa za'a yi jana'izarsa a garin Bauchi a gobe Juma'a idan Allah ya kaimu, inda ake sa ran babban Amininsa Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Alhusaini ne zai ma shi Sallah.

Marigayin dai ya rayu ne cikin neman ilimi da karantarwa inda yake da makarantu a lunguna da sako na fadin Najeriya, inda ya shekara 76 yana gudanar da tafsirin Alkur'ani mai girma.

Sheikh Dahiru Bauchi ya tafiyar da rayuwarsa wajen bayar da gudunmawa a fannin ilmin addinin Musulunci.

Sheikh Dahiru Usman Bauchi Yana da 'ya’ya 95 da jikoki 406 da tattaba-kunne 100. Daga cikin wannan adadin, ’ya’yansa 77 ne da jikoki 199 da kuma tattaba-kunne 12 ne suka haddace Alkur’anin mai girma. 


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: