Majalisar Dattawan Najeriya ta Amince da a rinka yanke hukuncin kisa akan masu garkuwa da mutane.
A ranar Laraba ne Majalisar Dattawa ta dauki matsaya mai tsauri kan matsalar rashin tsaro a kasar, inda ta ayyana yin garkuwa da mutane a matsayin ta'addanci tare da bayar da shawarar yanke hukuncin kisa ga duk Wanda aka samu da laifin, ba tare da zabin tara ba.
Kudurin dai ya biyo bayan cece-kucen da aka shafe sa’o’i ana tafkawa sakamakon harin da aka kai a cocin Christ Apostolic Church da ke Eruku a ranar 18 ga watan Nuwamba a karamar hukumar Ekiti ta jihar Kwara, inda ‘yan bindiga suka kashe wasu masu ibada biyu tare da sace wasu 38.
Duk da cewa daga baya an kubutar da dukkan wadanda harin ya rutsa da su a wani samame na hadin gwiwa da suka hada da sojoji, ‘yan sanda, jami’an DSS, da ’yan banga na yankin, ‘yan majalisar sun ce lamarin ya fallasa yadda gungun ‘yan tada kayar baya suka yi kaca-kaca a kudu da kuma durkushewar tsaro a yankunan karkara.
Matakin dai ya samo asali ne daga kudirin da Sanata Yisa Ashiru (Kwara ta Kudu) ya gabatar mai taken “Bukatar gaggawar magance matsalar rashin tsaro a Jihohin Kwara, Kebbi, da Neja da kuma karfafa tsarin tsaro na kasa,” wanda ya bude kofofin damuwa kan hare-haren da ake kai wa makarantu, wuraren ibada, manyan tituna, da daukacin al’umma.
Sanatocin sun yi nuni da cewa yawaitar sace-sacen makarantu ya sa aka rufe dukkan makarantun da ke kananan hukumomin da ke fadin jihohin Kebbi da Neja, da kananan hukumomi biyar a jihar Kwara, da kuma daukacin kwalejojin hadin kan gwamnatin tarayya guda 47 a fadin kasar.
Sanata Issa Jibrin (Kogi Gabashin Kogi) ya yi Allah wadai da matsalar karancin ma’aikata da ake fama da shi a kasar a fannin tsaro, inda ya yi gargadin cewa daukacin sojojin Najeriya da ‘yan sanda da jami’an tsaro ba su kai miliyan daya ba, idan aka kwatanta da miliyan 1.5 na kasar Masar.
Inda yayi kira ga Gwamnati ta yunƙura don samar da kayan aikin gaggawa da tallafawa sojojin da ba su da yawa.

0 Comments:
Post a Comment